KUBIYOMU KUSHA LABARI:Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Sifaniya, Real Madrid ta cika shekara 104 da take amsa sunanta. Da kuma kofunan datadauka atarihi...
Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Sifaniya, Real Madrid ta cika shekara 104 da take amsa sunanta.
Sarki Alfonso na takwas ne ya amince da sunan Real Madrid a wata wasiƙa da ya aike ranar 29 ga watan Yunin 1920.
An aike da wasikar daga wajen Sarki zuwa shugaban kungiyar, Pedro Parages ta hannun magajin gari, wadda ke kunshe da amincewar amsa sunan Real Madrid.
Wasikar na ɗauke da sakon cewar ''Mai martaba Sarki g.D.g na farin cikin amincewa da sunan Real (Sarauta) ga ƙungiyar ƙwallon kafa, wadda ta cancanci shugabancin kasa, daga yanzu wannan sunan za ake kiranta.
Ina sanar da ku wannan odar daga masarauta, domin fara amfani da wannan sakon.''
Wannan ya baiwa kungiyar damar nuna kambin sarauta a jikin rigarta, kuma daga wannan shekarar ne kungiyar kwallon kafa ta Madrid ta canza sunanta zuwa Real Madrid.
Kofunan da Real Madrid ta ɗauka a tarihi
Real Madrid ce ta lashe Champions League na kakar da aka kammala na 15, kuma ita ce ta ɗauki La Liga na 36 jimilla.
Real ta yi nasarar cin Champions League na bana, bayan da ta doke Borussia Dortmund da cin 2-0 a Wembley.
Haka kuma ita ce ta ja ragamar teburin La Liga a kakar da ta wuce da mai 95, yayin da Barcelona ta yi ta biyu da maki 85 da Girona ta uku mai maki 81.
La liga 36
Spanish Cup 20
Spanish Super Cup 13
Champions League 15
Fifa Club World Cup 8
European Super Cup 5
Uefa Cup 2
The Best Club of 20th Century Fifa Trophy 1
