Abin takaici an kama wannan matar mai suna Aisha Abubakar ta ɗauko harsashin bindiga sama da guda dubu biyu daga Abuja zata kaiwa ɓarayin daji, ƴan ta'adda masu garkuwa da mutane a garin Ƴantumaki ƙaramar hukumar Ɗan-Musa a nan jihar Katsina
Wallahi ana cutar damu abun ban haushi da takaici, wai yanzu ace da mutanenmu za'a dinga haɗa kai domin wargaza zaman lafiyarmu?, kuma mutanen mata ba maza ba, mata da aka sansu da tsananin tausayi da jin kai, domin zaku ga yanzu matane akafi kamawa suna kaiwa baryin daji makamai
Tabbas Hakan ya ƙara tabbatar wa, duk taddancin da ɓarayin daji ke yi akwai gurɓatattun mutane a cikinmu da suke taimaka musu don kawai su samu kuɗi, don haka matsalar yaƙi da ƴan bindiga ba wai laifin Gwamnati bane kaɗai, yanzu wannan da ace ta samu nasaran isar da alburusan ga ƴan bindiga Allah kaɗai Ya san ɓarnan da za'ayi da su, don haka jama'a a cigaba da bawa jami'an tsaro haɗin kai da bayanan sirri
Kamar yadda zakuji matar ta faɗa da bakinta, tace wai yunwa ne ya sakata aikata wannan mummunan aiki, kuma wai shine karo na farko, akwai cikakken bidiyo na tambayoyin da aka mata tana amsawa a Comment Section nawa 👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
Amma ni ba zan taɓa yadda da uzurin yunwa ba, ace mutum saboda yunwa zai je ya aikata laifi mai muni irin wannan, wanda za'a kashe ƴan uwansa da shi
Allah Ya sauwaƙe, Ya kawo mana ƙarshen wannan masifa Ameen ya hayyu ya quyyum 🙏🙏🙏🙏
Ya Allah kakaratsare AL'FARMAR ANNABI MUHAMMAD S A W.🤲🤲🤲