KATSINA STATE AYAU

                  KATSINA STATE AYAU

Jihar Katsina ta lashe kyautar "Best State Health Insurance Agency of the Year 2024" wato: Jiha Ma fi tsarin da kyan Hukumar Inshora ta lafiya a shekarar 2024.

Jihar Katsina ta lashe kyautar ne a taron "National Healthcare Excellence Awards," wanda ya zama nasara ta biyu a jere bayan shekarar 2022.

Wannan ya nuna da kuma tabbatar da jajircewar jihar kan kiwon lafiya a karkashin Gwamna Malam Dikko Umaru  Radda, wanda yayi tanadi da sabbin tsare-tsare a kan kiwon lafiya a kowane mataki, yadda kowa zai samu dama, da kuma kiwon lafiya a arha. 

Gwamna Radda ya mika godiyarsa ga dukkan masu ruwa da tsaki, ya kuma kara nunawa da bayyana aniyarsa na ganin an samu nagarta a fannin kiwon lafiya, tare da yin aiki donci gaba da inganta fannin a jihar.

Gwagware Online Vanguards

22/06/2024



Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form