SARKIN MALAMAI MEDIA TEAM KATSINA STATE
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa PhD CON ya amshi tawaga mai ƙarfi daga Hukumar UNDP a Filin Jirgin Ƙasa da Ƙasa na tunawa da Marigayi Malam Umaru Musa Ƴar'adua dake Katsina.
Tawagar UNDP tazo Katsina ne domin halartar Babban Taron Masu Ruwa da Tsaki na Shiyyar Arewa maso Yamma domin tattaunawa akan matsalar Tsaron data addabi yankin.
Hakanan kuma tawagar UNDP ta samu jagorancin Babban Wakilin Hukumar ta Ƙasa Nigeria, Mr. Attafuah.
Wannan ya nuna jajir cewar Gwamna Raɗɗa akan magance matsalolin tsaron dake addabar Jihar Katsina, Yankin Arewa maso Yamma dama Ƙasa baki ɗaya.
Rabiatu Sulaiman Kurfi
S.A Digital Media to
Katsina State Governor
Shared by Pharm Yarima Angawa Chairman for Sarkin Malamai Media Team Katsina State..