KUBIYOMU ASHAFINMU DOMINJIN WANI LABARI SHAHARARREN DAN BINDIGANNAN WANDA YAYIKAURIN SUNADOGO GIDE WAI YAKOMA BAIWA MANOMA KARIYA DON SU KOMA GONA A JAHOHIN AREWA RIIHOTO DAGA BBC HAUSA A NIGERIA SHIN KOMIZAKU IYACEWA DANGANE DAWANNAN AL'AMARI MUHADU A COMMENTS SECTION......

 KUBIYOMU ASHAFINMU DOMINJIN WANI LABARI SHAHARARREN DAN BINDIGANNAN WANDA YAYIKAURIN SUNADOGO GIDE WAI YAKOMA BAIWA MANOMA KARIYA DON SU KOMA GONA A JAHOHIN AREWA RIIHOTO DAGA BBC HAUSA A NIGERIA SHIN KOMIZAKU IYACEWA DANGANE DAWANNAN AL'AMARI MUHADU A COMMENTS SECTION.........


Daga BBC Hausa 

A wani al'amari mai ban ta'ajibi fitaccen ɗan bindigar nan da ya yi ƙaurin suna wajen addabar jama'a a arewacin Najeriya Dogo Giɗe, yanzu ya fara ba wa manoma kariya don su koma gonakinsu a jihar Zamfara.

Manoma a ƙananan hukumomin Tsafe, da Maru da ke Zamfara, da ma wani ɓangare na yankin ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina, sun shaida wa BBC cewa sun zauna da Dogo Giɗen, kuma ya musu alkawarin kare su daga sauran gungun ƙungiyoyin ƴan bindigar da a baya suka hana su noma a gonakinsu.

Majiyoyi sun shaida wa BBC Hausa cewa riƙaƙƙen ɗan bindigar ya koma gida Zamfara ne bayan dakarun Najeriya sun yi luguden wuta tare da lalata gidansa, da komawarsa ne kuma ya gargaɗi kungiyoyin ƴan bindigar da ke wadannan yankuna su daina kai wa jama'a hari da hana manoma noma, idan kuwa ba haka ba zai hakala su.

Wani mazaunin yankin da ya yi magana da BBC ya ce ''Yana can gefen Babbar Doka da ke karamar hukumar Maru, iyayensa ne suka roke shi ya koma gida bayan harin da sojojin Najeriya suka kai gidansa, bayan ya koma ne ya yi wa sauran wannan kungiyoyin yan bindiga gargaɗi, yanzu haka ana zaune lafiya, manoma sun koma gona ba wata matsala, daga Magami za ka tashi ka tafi har Taketa, babu wata matsala, Dogo Gide na kare jama'a''

Ya ƙara da cewa ''garuruwa da dama kamar Madaba, da Kabasa, da Yar zega, da Sabon garin Dutsen Kura, da Munhaye, duka manoma sun koma gona, sannan lafiya lau ake zaune har dare ana yawo kamar yadda ake a baya''

Shima wani mazaunin garin da ke cikin waɗanda suka zauna da madugun ƴan bindigar Dogo Giɗe, ya shaida wa BBC cewa ''Mun zauna da shi, ya mana alkawari, kuma mun tabbatar, tunda inda ba ma zuwa shekara biyar baya yanzu muna zuwa, ana zuwa ana noma, ana huɗa ana shuka, idan ma kwana kake so ka yi a daji za ka iya, ni kaina na yi shuka a gonata, yaransa suna zagayawa kuma gaba ɗaya wadanda suke addabar jama'a yanzu sun gudu.

Ya ci gaba da cewa Dogo Giden ya shaida masu cewa ba ya buƙatar kudinsu.

Da muka tambaye shi ko ya shaida masu cewa ya tuba ne ?, sai yace bai sanar da su hakan ba.

"Abun da ya ce mana shine halin da al'umma suke ciki shi ne abin da ya dame shi don haka kowa ya je ya ci gaba da harkokinsa na noima abin da zai ci.

'A tsaya a ga iya gudun ruwansa'

Wannan al'amari dai ya ba wa hatta masu nazartar lamuran yan bindigar a arewacin Najeriyar mamaki, Mannir Sani Fura Girke, wani ɗan jarida mai binciken kwakwaf kan harkar yan bindigan ya ce abun da Dogo Giɗen ya yi, sabon ci gaba ne, sai dai akwai bukatar mahukunta su saka ido sosai.

"Ya kamata gwamanti ta saka ido a ga shin da gaske yake ya tuba ko kuwa, kuma ya ajiye makaman sa ya sallamawa gwamnati, idan har hakan ta tabbata na san gwamnati za ta so hakan domin zai kasance wani gagarumin ci gaba'' inji shi.

Matsalar tsaron da ake fama da ita a arewacin Najeriya dai ta haifar da gagarumin koma baya ga bangarori da dama, daga ciki har da noma, wanda aka san yankin da shi.

A garuruwa da dama yan bindiga kan hana manoma zuwa gonakinsu har ta kai kai ga suna kai musu hari suna hallaka su, a wasu wuraren kuma a tursasa musu biyan haraji.

Dogo Gide, na daga cikin wadanda ake zargin sun shafe shekaru suna yin hakan, kafin wadannan rahotanni na baya bayan nan.


Allah kakaratsaremu da tsarewarka..


Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form