Ƙasashen da aka fi kwankwaɗar barasa a duniya

 Ƙasashen da aka fi kwankwaɗar barasa a duniya...


Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ce mutum miliyan 2.6 ne ke mutuwa sakamakon kwankwadar barasa a kowace shekara.

WHO ta ce shan giya na ƙara hatsarin kamuwa da munanan cututtuka kamar ciwon zuciya da hanta da kansa da kuma taɓa lafiyar kwakwalwa.

Hakan na kunshe ne a wani sabon rahoto da hukumar ta fitar kan shan giya da lafiya da kuma kulawa ga masu shan miyagun kwayoyi.

Rahoton ya yi ƙiyasin cewa mutum miliyan 400 ne ke rayuwa da shan barasa da wasu ƙwayoyi da ke gusar da hankali.

''Daga cikin wannan adadi mutum miliyan 209 ne suka dogara da shan barasar domin rayuwa'', in ji rahoton.

Shugaban Hukumar Lafiyar ta Duniya ya ce shan barasa na matuƙar cutar da lafiyar mutane da kuma haifar da illoli masu yawa ga mutanen da suka fi shan barasar.

"Dole ne mu tashi tsaye don kawar da shan barasa, idan muna son inganta lafiya da walwalar al'ummarmu'', in ji shugaban na WHO.

Rahoton ya kuma nuna cewa ƙasashen da ke yankin nahiyar Turai ne kan gaba wajen kwankwaɗar barasa, inda aka yi ƙiyasin cewa matsakaiciyar barasar da mai shan giya ke sha a kowace shekara ta kai lita 9.2.

Sai kuma yankin nahiyar Amurka inda duk mashayin barasar kan sha mai yawan lita 7.5 a kowace shekara.

1. Romania

Ƙasar Romania da ke yankin kudu maso gabashin haniyar Turai ce ke kan gaba wajen yawan mashaya giya kamar yadda alƙaluman WHO suka nuna.

Romania mai yawan al'umma miliyan 19.12, ta yi fice wajen tara mashaya giya.

2. Georgia

Georgia - wadda ke cikin tsohuwar tarayyar Soviet da ta wargaje - na tsakanin yankunan Turai ta Asiya.

Ƙasa ce mai yawan al'umma kimanin miliyan 3.8 mai ɗimbin tarihin al'adu da wadda kuma ta yi fice wajen kwankwaɗar barasa a duniya.

A baya kundin adana abubuwan tarihi na Guinness ya taɓa sanya ƙasar a matsayin wadda ta fi sarrafa barasa a duniya.

3. Jamhuriyar Czech

Alƙaluman na WHO sun ayyana ƙasar Jamhuriyar Czech a matsayin ƙasa ta uku mafi shan barasa a duniya.

Haka kuma ƙasar ce ta farko da ta fi kashe kuɗi a kan barasa a duniya, inda a shekarar 2019 rahoton alƙaluman ƙididdiga na Turai ya nuna cewa ƙasar ta kashe kusan dala biliyan huɗu kan barasa.

Rahoton na WHO ya kuma nuna cewa mafi yawan mutanen da mutuwa sakamakon shan barasar na mutuwa ne saboda shan gurɓatacciyar barasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form