DA ƊUMI ƊUMI: An Fitar Da Jadawalin Yadda Zanga-zanga Zai Kasance Acikin Garin Malumfashi

 DA ƊUMI ƊUMI: An Fitar Da Jadawalin Yadda Zanga-zanga Zai Kasance Acikin Garin Malumfashi 


(1)- Tsarin fitowarmu Zanga zanga" karfe 6:00Am na safe.


(2)- Alummar yankin 

G,G bye pass Zasu Rufe hayar zariya da kafur 6:00am na safe.


(3)- Alummar dake Unguwar mata Zasu Rufe hanyar dayi Road zuwa malunfashi. 6:00am na safe.


(4)- Alummar  dake hayin gada  zasu Rufe Hanyar funtua xuwa malumfashi  6:00am na safe

 


DOKA! DOKA!! DOKA!!!


(1)- Babu mākāmî.

(2)- Babu taba kayan kowa.

(3)- Babu fada ku cin zarafin wani.

(4)- kowa ya fito da rubutu na kokensa a jikin kwali.


Taimako! Taimako!! Taimako!!!


(1)- masu halin cikinmu  su dafo abinci.

(2)- wasu su taimako da ruwan sha da kuma magani.

(3)- mu taimaki duk wanda yake bukatar taimako ko wana iri" uwa daya uba daya.


Bamu daukewa kowa ba" daga kan Dan shekara 18 zuwa sama" matasa maza da mata" Dattijai da tsofaffi" kowa ya fito domin ceto kasar mu daga halin da shugabanni suka jefata na tsananin yunwa da tsadar  rayuwa da kuma  rashin tsaro.


ABINDA MUKE BUKATA SHINE,


(1)- A bude bodojin Arewa baki daya domin ashigo da abinci kamar yadda yake a baya da kuma kaiyade masa farashi.


(2)- A dawo da tallafin man Fetir ya dawo 200 duk lita.


(3)- Duk yan kunan dake fama da rashin tsaro a Arewa a dawo da zaman lafiyar yankin domin cigaba da noma da kiyo.


(4)- A dawo da tallafin karatu domin Dan Talaka ya yaki Jahilci.


(5)- A samarwa matasa maza da mata aiyukan dogaro dakai domin gujewar aikata munanan laifuka.


(6)- A dawo da tallafin wutar lantarki, domin karfafar masana'antu manya da kanana


Lokacin fitowa karfe 6:00Am na safe zuwa 60:00Pm na yamma. 


Kafin afito kowa ya karanta duk wata addu'a wanda ya iya domin neman taimakon Ubangiji ya bamu ikon fita lfy mu dawo lafiya..



Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form