Kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar Sun Dakatar Da Amfani Da Fasfo Ga Junansu.
Daga Wakilinmu
Kashen kawancen juna wadanda ke Mulkin Soji a Afirka, AES sun yanke shawarar matakin dakatar da Fasfo da kuma katin kasa wadda ake kira da biometric na ECOWAS a tsakaninsu.
Kashen AES da suke su Uku wadanda suka hada da Burkina Faso, Mali da kuma Nijar, za su dakatar da aiki da Fasfo da Katin dan kasa a yayin ga al'ummomin kasashen a duk sadda za su mu'amalanci daya daga cikin kasashen Uku, Zamani Media Crew ta ruwaito.
Kasashen sun amince da wannan kudirin a yayin wata ganawarsu a karshen makon nan a wani mataki da kara kusancin kawancensu a matsayinsu na kashen masu aiwatar da Mulkin Soji.
Sun ce a bisa ka'ida dokar dakatawar za ta ta fara aiki ne daga farkon sabuwar shekara mai zuwa ta 2025
Wannan dai na daya daga cikin matakin da kasashen 3 suka dauka na ficewa daga kungiyar ta ECOWAS, tun bayan da suka zama kashe masu gudanar da Mulkin Soji.