LABARIN WASU MASOYA....

 LABARIN WASU MASOYA.....

Labarin wasu masoya ne zan baku da fatar zaku fahimce ni.

Sudai wadannan masoya sun kasance daga farkon soyayyar su,kamar ‘yan biyu ne koda yaushe suna tare,suna fadawa juna maganganun soyayya har ma da dariya,basu son abinda zai sosa ran daya.soyayya tayi karfi sosai har alkawarin aure ya shiga tsakaninsu,saboda sun yarda da junansu fiye da kima.To shidai yaron dan talakawa ne.Gidansu ba masu wadata bane,amma duk da haka ta nuna ta amince dashi,ya kamu da kaunarta kauna mai tsanani.Ana cikin haka sai chanji ya shiga.masu kudi da manyan motoci suka fara farautarta kuma wani daga cikin ya samu amincewarta,dan shi babban dan kasuwa ne kuma yanada kudi.Ya aureta yakai gidansa.

Allah (SWA) ya arzuta ta da juna biyu har ya kai wata ukku,sai ya fara jin ya gaji da ita,karshe dai ya sake ta saki (3) ta koma gidansu tana kokawa da kannenta wajan cin abinci,rayuwarta ta lalace.

Shi kuma tsohon saurayin nata Allah ya bashi wadata bayan ta auri mai kudi,shi kuma duk da yana talaka sai wani attajiri ya bashi ‘yarsa,kuma tafi ta kyau.wannan kenan,Dan Allah mu kiyaye maza da mata mu daina sanya kwadayi cikin harkar aure dan gudun afkawa cikin wahala...



In kunne yaji,gangar jiki ta tsira.

07038375607,

08058272218.

thanks

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form