Yadda ‘Cousin’ Ke Kawo Tarnaki Ga Masoya...
Wasu na ganin kozin na tafka aika-aika idan ba a yi masa shinge tsakaninsa da 'yar uwarsa ba.K
a taba jin labarin wadanda daga wasan yaya da kanwa (wato Cousins a turancin Ingilishi) suka rikide zuwa masoya, suka aure miji ko budurwa ko saurayin wata?
Zara Muhammad, ta ba mu labarin yadda daga kanwa da yaya, sahibinta ya narke cikin kogin son ’yar innarsa, ya bar ta da ciwon zuciya.
A cewar Zara, da farko ba ta yi zaton wata soyayya, ballantana ma mai karfi na iya shiga tsakanin masoyin nata da cousin dinsa ba.
Amma gararin da Cousin din sahibinta da ta yi mata kutse ta kwace shi, ta jefa ta, da irin kwakwar da ta ci kafin ta samu ya dawo gareta, ya sa take kaffa-kaffa da duk wata Cousin dinsa, domin kada a koma gidan jiya..
Cousin kalma ce ta Ingilishi da ke nufin dan kawu, dan inna, dan goggo ko dan baffan mutum — wadanda ake kira abokan wasa a al’adar Bahaushe.
Yaya kuke ji a ranku idan kuka ga ana dasawa tsakin rabin ranku da Cousin dinsu da ba jinsinsu daya ba?
Sanannen abu ne cewa zamantakewar soyayya da aure aba ce da ta da ke mamaye zuciya, har ta sanya begen juna, musamman idan ta kasance cike da nuna wa juna kulawa da kauna da tausayi da sauransu.
Shi ya sa rabuwa da masoyi ko idan ya juya wa masoyinsa baya, yake shiga damuwa, wani lokaci har da rashin lafiya.