Shugaban ya ce ya damu ƙwarai da damuwar al'ummar ƙasa kuma zai mayar da hankali a kai..
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu lokacin da yake gaisawa da Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar 25 ga watan Yuli, 2024
- Ibrahim Haruna Kakangi
- BBC, Abuja
Lokaci na ci gaba da matsowa game da zanga-zangar da wasu matasa ke shiryawa a Najeriya, wadda suka ce za su yi ne domin nuna fushinsu kan matsin rayuwa da rashin tsaro.
Sai dai yayin da matasan ke nasu shirin, gwamnatin Najeriya ita ma tana nata.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi jerin ganawa da kusan duk masu faɗa a ji a ƙasar a ƙoƙarin janyo hankalin matasa wajen ganin su jingine shirin nasu na yin zanga-zanga.
Wannan baya ga sauran ganawa ke nan da sauran manyan jami'an gwamnati suka yi a ƙoƙarin nemo hanyoyin da za a lallashi matasan su janye ƙudurinsu na yin zanga-zanga.
Misali, sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu sun jagoranci wani taro da ministocin gwamnatin Tinubu a ranar Laraba game da batun.
Haka nan Tinubu ya umarci gwamnoni su koma jihohinsu domin ganawa da mutane tare da lallashin su kan batun zanga-zangar.
BBC ta duba wasu daga cikin muhimman masu ruwa da tsaki da shugaban na Najeriya ya gana da su game da batun zanga-zangar:
1- Sarakunan Gargajiya
Na gaba-gaba a cikin waɗanda shugaban ƙasar ya tattauna da su a ranar Alhamis su ne sarakuna daga sassan ƙasar.
A cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar, ta ce a lokacin tattaunawar, Shugaba Tinubu ya ce ya damu ƙwarai da damuwar al'ummar ƙasa kuma zai mayar da hankali a kai.
Waɗanda suka halarci ganawar sun haɗa da Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar da Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.
Haka nan akwai sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli, da Etsu Nupe, Yahaya Abubakar da ma wasu da dama.
Ganawar da Tinubu ya yi da sarakuna ba zai rasa nasaba da kallon da ake yi wa sarakuna a matsayin iyayen al'umma ba.
Suna daga cikin masu faɗa a ji tsakanin al'umma, kuma ana ganin cewa zai iya yiwuwa abin da za su faɗa wa mabiyansu ya taimaka wajen kwantar da hakali tare da hana faruwar zanga-zangar.
2 - Malaman addinnin Musulunci
Wani rukunin al'umma da shugaban ƙasar na Najeriya ya gana da su, su ne malaman addinin Musulunci daga bangarori daban-daban.
A lokacin ganawar da ta gudana ranar Alhamis, kusan abu ɗaya ne Tinubun ya shaida musu kamar yadda ya shaida wa sarakuna.
Sai dai malaman sun ce ya ba su dama su faɗa masa ƙorafe-ƙorafensu.
Sun ce sun nuna wa shugaban irin tsanani da damuwa da jama’a ke ciki, inda suka gabatar masa da wasu shawarwari kan yadda gwamnati ta za ta bi domin sama wa jama’a sauki.
"Shugaban ƙasa ya saurare mu kuma ya ce a ja hankalin al'umma su ƙara haƙuri... a yi haƙuri, nan gaba kaɗan za a ga canje-canje cikin waɗannan ƙorafe-ƙorafe da muka kawo," in ji shugaban ƙungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'ah wa Ikamatus Sunnah, na Najeriya, Sheik Abdullahi Bala Lau.
Su ma malaman addini, kamar sarakuna, mutane ne da ke da ɗimbin mabiya, kuma maganganunsu na tasiri a cikin al'umma.
3 - Gwamnonin Jam'iyyar APC
Tun farko a ranar ta Alhamis, shugaba Tinubu ya yi wata ganawa da gwamnonin jam'iyyar APC.
Bayan kammala taron ƙungiyar gwamnonin na APC ta ce ba ta san dalilin da ya sa wasu ƴan Najeriya ke shirin gudanar da zanga-zanga ba.
A jawabi a taron manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron ƙungiyar a Abuja, babban birnin ƙasar, shugaban ƙungiyar - wanda shi ne gwamnan jihar Imo, Hope Udozinma - ya ce ''mu ba mu san dalilin da ya sa suke shirin yin zanga-zangar ba, inda mun sani za mu gayyace su don zama da su domin samun maslaha''.
Haka nan gwamnonin sun yi kira ga ƴan Najeriya su yi haƙuri tare da bai wa gwamnati ƙarin lokaci.