Tsakanin Su wayafi lefi? Amma saikakaranta : Tana kwance akan shimfiɗar ajali, ta cewa mijinta,
ka gafarta mini...! Ya ce babu komai!
Ta ce, dukkan rigimar da ta faru tsakanin Kai da Mahaifiyarka ni na kunnata. Ya ce, babu komai, na yafe miki...!
Ta ce, ƴan uwanka da suka tsane ka, ba sa son ganinka duk ni na shiga tsakaninku. Ya ce, kar ki damu, duk na yafe...!
Ta ce, basussukan da na jefa ka, da kuma faɗa tsakaninka da abokan aikinka ka yi haƙuri..!!! Ya ce, komai ya wuce, ki daina tunawa...!
Matarka daka rabu da ita ni na shiga tsakaninku kuma ni na saka Alƙali ya turaka gidan gyaran hali....! Ya ce, na yafe, Allah mai gafara ne kuma mai jin ƙai...!!!
Ya ce, nima ki yafe mini.....!!! Ta ce, baka yi mini komai, ai kai Waliyi ne, in ma akwai, sai dai bisa kuskure, kuma na yafe maka Duniya da Lahira.
Ya ce, na san duk abin da kika aikata, shi yasa na baki Shayi da GUBA a ciki.......!!!!!
Shin ko Wane darasi kuka dauka....
