Da dumi dumi An Dage Sauraron Karar Shari'ar 'Ya'yan Jam'iyyar APC Da Ganduje Kubiyomu kaji cikakkaken Labari.

 


An Dage Sauraron Karar Shari'ar 'Ya'yan Jam'iyyar APC Da Ganduje Kubiyomu kuji cikakkaken labari

Daga Moh'd A. Isa.

A zaman da babbar kotun tarayya mai zamanta a Abuja ta yi a ranar Larabar nan, ta sanya ranar 5 ga watan Yulin 2024 domin ci gaba da sauraron karar da aka nemi sauke shugaban Jam'iyyar APC na kasa mai ci, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Mai shari'a Inyang Ekwo ne ya daga zaman zuwa waccan rana, domin bai wa masu kara damar martani kan ƙorafin tsohon gwamnan na Kano kuma shugaban Jam'iyyar APC ta kasa, Ganduje.

Kungiyar 'ya'yan Jam'iyyar APC a shiyyar Arewa ta tsakiya dai ne, suka kalubalanci Ganduje a kotu, kan cewar nadin da aka yi masa a matsayin shigaban jam'iyyar ya saba wa kundin Mulkin jam'iyyar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form