Ayau ne ake zaman sauraron ra’ayin jama’a kan gyaran dokar masarautu a Sokoto.....
Sa'o'i 8 da suka wuce..
A yau Talatar nan ne kwamitin da Majalisar Dokokin jihar Sokoto ta miƙa wa ƙudurin dokar gyaran fuska ga masarautu zai fara zaman sauraren ra’ayin jama’a game da dokar da ta shafi ƙanannan hukumomi da masarautu.
Tun da farko gwamnatin jihar ta ce zai yi gyara ne ga sashe na 76, kashi na biyu na dokar ƙananan hukumomin jihar ta shekarar 2008.
An riga an yi wa dokar karatu na farko da na biyu a wani zama da aka yi ranar Talatar makon jiya, inda ake sa ran da ƙudurin ya zama doka, ƙarfin ikon nadawa da cire hakimai da dagatai zai koma ƙarƙashin ikon gwamnan jihar Sokoto, maimakon Sarkin Musulmi.
Dokar ta shafi damar da Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na uku ke da ita, kan naɗa hakimai da dagatai kai tsaye, inda ikon hakan zai koma hannun gwamnan jihar da zarar dokar ta tabbata.
Sai dai lamarin na ta haifar da ce-ce-ku-ce, inda jama’a da dama a Najeriya suka bayyana matakin da shirin rage ƙarfin ikon Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku.
Daga cikin waɗanda suka mayar da martini har da ƙungiyar Muslumi ta Najeriya Muric, da ta bayyana cewa taɓa kimar Sarkin Musulmin tamkar taba ruhin Musulman Najeriya ne.
Haka kuma, a cikin jawabin da ya gabatar ranar Litinin ta makon jiya, a wajen taro kan matsalar tsaron da ke addabar jihohin arewa maso yammacin Najeriya, mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima shi ma ya ce dole ne a kare martabar Sarkin Musulmin.
Wannan ma ya jawo wasu ‘yan majalisa na ɓangaren jam’iyya mai hammaya ta PDP a jihar suka bayyana cewa babu wani muhimmanci ga sabuwar dokar face wata manufa ta bi-ta-da-kulli irin na siyasa.
A cewarsu, gwamnatoci da dama sun bar dokar a yadda take cewa Sarkin Muslumi ne mai alhakin nadawa da cire sarakuna da hakimai da ke ƙarƙashin ikonsa, ba gwamnan jiha ba.
Sai dai a wani martani da ta mayar, gwamnatin jihar ta Sokoto ta ce dokar da aka yi wa karatu na farko da na biyu da kuma aka miƙa ga kwamitin da zai gudanar da sauraren ra’ayin jama’a a ranar Talatar nan ba ta da wata manufa face mayar da tsarin naɗin hakimai da dagatai zuwa yadda ya kasance tun fil-azal.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Sambo Bello Danchadi ya ce: “Dokar kawai za ta sake dawo da tsarin da ake amfani da shi ne a gomman shekaru da suka gabata..