Me zai faru idan Donald Trump ya lashe zaɓen shugaban Amurka?
A karkashin dokar Nato, duk wani hari a kan mamba guda na kungiyar tamkar hari ne ga kungiyar baki daya.
Amma a watan Fabarairun wannan shekarar Trump ya ce ba zai kare kasar da ba ya biyansu ba kuma zai ci gaba da karfafawa Moscow.
American (left) and Nato flags are seen flying together in Warsaw on 12 April 2024ASALIN HOTON,GETTY IMAGES
Ana ci gaba da samun mabanbanta ra'ayi kan ko zai janye alakar Amurka da ƙawayenta.
Amma Ed Arnold daga cibiyar bincike ta Landan ya ce yana iya yi wa aikin nasu zagon kasa ba tare da ja fidda Amurka ba, ta hanyar kara yawan sojojin Amurka a Turai a kuma kakaba dokoki mai tsauri kan batun Rasha da Ukraine.
Trump ya sha alwashin tasa ƙeyar baƙi
Shugabancin Trump na tattare da ce-ce-ku-ce kan tsare-tsarensa na baki, kuma ya alkawarta sake tsawwala yanayi da zarar ya hau mulki.
Ya ce a wata rana zai aiwatar da gagarumin shirin mayar da kowane bako gida domin kafa tarihi a Amurka.
A group of migrants wait in line near a US Border Patrol field processing centre after crossing the Rio Grande from Mexico on 18 December 2023 in TexasGETTY IMAGES
A lokacin da yake kan mulki, Trump ya haifar da zazzafan rikicin kasuwanci da China. Ya ce idan aka sake zaben sa, zai kakaba wa kasar harajin sama da kashi 60 cikin 100.
A bara ya yi wasu kalamai masu tsauri kan makomar China da yadda zai dakushe ta a kowanne fanni kama daga gine-gine da makamashi da sadarwa.
Yayin da ake ci gaba da fuskantar tashin hankali a kudancin China da kuma kan Taiwan, wasu na fatan ganin tsare-tsaren Amurka na tsaro sun mayar da hankali kan China.
Taiwan yanki ne mai cin gashin kai da ke ganin babu alaka tsakaninsu da China, saboda tana da kundin tsarin mulkinta da gudanar da zaben shugabanninta.
Sai dai Beijing na musu kallon wani yanki nata da ke bore kuma tana ganin za ta mayar da ita kan hanya.
Amurka karara ba ta fito ta bayyana yadda za ta yi ba ko mataki idan China ta mamaye Taiwan, kodayake Mista Biden a kullum kalmarsa ita ce Amurka za ta kare kanta.
Trump dai yaki ambata abin da zai yi. Sai da ya taba tunzura China a zaben 2016, lokacin da ya karbi sakon taya murna daga shugaban Taiwan.
Ina batun muhalli?
A matsayinsa na shugaban kasa, Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyara sauyin yanayi ta Paris ta 2015. Mista Biden ya sake waiwaye a kai - amma shafinsa na gangamin yakin neman zabe na cewa zai sake ficewa.
Sannan shafin ya ce zai hana wasu ayyukan danyen mai da ke gurbata muhalli irin su rage haraji ta fannin mai da iskar gas da gawayi da wasu tsare-tsare da Mista Biden ya bijiro da su.
Emissions rise from a coal-fired power plant in the US state of West VirginiaASALIN HOTON,GETTY IMAGES
Dr Simon Evans, mataimakin editan shafin da ke sa ido kan sauyin yanayi na Carbon Brief, ya ce da wuya Amurka ta cimma yarjejeniyar kasashen duniya kan sauyin yanayi da zarar Trump ya koma kan mulki.
Mista Biden ya zuba dala bilyan 300 wajen bunkasa da kawo sauyi a fanin makamashi mai tsafta da kawar da abubuwan da ke gurbata muhalli.
Sai dai akwai masu fafutukar kare muhalli da ke adawa da shirin, suna mai cewa ana dai sake habaka harkar danyen mai da iskar gas ne.
Ana ganin Biden na iya kokarinsa, a cewar Dr Simon.