Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya IGP Kayode Egbetokun, ya halarci taron tsaro da zaman lafiya na yankin Arewa maso Yamma da aka gudanar a Katsina.
Inda ya bayyana irin kokarin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ke yi na tabbatar da doka da oda a yankin. Ya kuma jaddada kara kaimi wajen yaki da ‘yan fashi da garkuwa da mutane da ta’addanci, ya kuma yaba da jajircewa da kwarewar jami’an ‘yan sanda.
IGP din ya kuma jaddada mahimmancin aikin ‘yan sandan al’umma da ayyukan soji na hadin gwiwa, wanda ya kai ga samun nasarar shiga tsakani da inganta tsaro.
Duk da kalubalen da ake fuskanta, ya yi kira da a samar da cikakken tsarin tsaro, wanda ya yayi dai-dai da sabon tsarin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya kuma karfafa gwiwar mahalarta taron da su bullo da dabarun inganta tsaro, tsaro da walwala a yankin Arewa maso Yamma.
Gwagware Online Vanguards
25/6/2024