Gwamnoni basu fahimci dokar mafi ƙarancin albashi ba - NLC....
Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya, ta mayarwa da wasu gwamnomin jihohin ƙasar martani kan ƙoƙarin da suke na ganin an bai wa kowacce jiha damar yanke abin da za ta iya biya a mastayin albashi mafi ƙaranci, saɓanin ƙokarin da ake yi na ganin an amince da farashi na bai ɗaya.
Kwamared Benjamin Anthony, mataimakin shugaban ƙungiyar ƙwadagon ta Najeriya, ya shaida wa BBC cewar albashi mafi ƙanƙanata ake son a biya, wanda kuma a duniya ma idan aka kayyade albashin mafi ƙaranci da za a biya, babu wani sashe ko jiha da za ta biya ƙasa da yadda aka ƙayade, tunda doka ce ta bai ɗaya, wadda ita kanta ƙungiyar ƙwadago ta duniya ta amince da ita.
Kwamared Benjamin Anthony, ya kara da cewar “rashin adalci ne da ake fama da shi a kasar, a ce ga gaskiyar abin da tattalin arziki ke cewa, a ce ga albashi mafi karanci da za a biya, amma a ce ba za a bi ba, ko da gwamnati ta ce zata bayar da naira dubu sittin da biyu (N62, 000) mun yi tambayar nawa ne kudin mai a ciki ?, nawa ne kudin mota nawa ne kudin makaranatar yara?, nawa ne kudin haya? inji shi.