Kubiyomu Kusha Labari Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa PhD CON Shugaban Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Yankin Niger Delta (NIGER DELTA POWER HOLDING COMPANY).
Wannan Shugabanci ya samu amincewar Majalissar Zartarwa ta Ƙasa mai kula da Tattalin Arziƙin Ƙasar nan, a inda Majalissar ta bayyana cewa, hakan na daga cikin manufofin Gwamnatin Tarayya na inganta harkokin samar da Wuta musamman a yankin.
Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa PhD CON na daga cikin Gwamnoni Shidda da aka zaɓa domin Wakiltar Shiyyoyi daban daban na Ƙasar nan.
Sauran Gwamnonin sun haɗa da na Borno, Imo, Ekiti, Kwara da kuma na Jihar Akwa Ibom.
Shi dai wannan Kamfani na samar da wutar lantarki na Yankin Niger Delta yayi rijista da Gwamnatin Tarayya da sauran Hukumomi, kuma mallakin Gwamnatocine na Tarayya, Jahohi, da kuma Ƙananan domin cike giɓin samar wuta a yankin.
Da yake magan tawa jim kaɗan bayan amince wa da Shugabancin Hukumar, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa PhD CON ya godema Shugaba Tinubu akan amincewa da shi akan wannan jagoranci, sai ya tabbatar cewa, zaiyi dukkan abinda ya dace domin inganta harkokin samar da wutar lantarki a Yankin.
Ya kuma roƙi sauran mahukuntan Hukumar da su haɗa hannu da shi domin cigaban Yankin dama Ƙasa baki ɗaya.
Gwamna Raɗɗa ya kuma nanata cewa, zai sa dukkan basirar shi da jajircewar duk data kamata domin cigaban Hukumar...
Abubakar Bala Funtua
S.A Digital Media Funtua Zone,
To Katsina State Governor.
28/6/2024