Rana ta biyu Taron tabbatar da Tsaro da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.
Yau ne Rana ta biyu a Taron zaman lafiya da yake gudana a jihar katsina wanda gwamnonin yankin Arewa maso yammacin Najeriya tare da majalisar Dinkin Duniya suka dauki nauyin gudanarwa.
Maigirma Ministan gidaje da Raya Birane na Najeriya Arch Ahmed Musa Dangiwa tare da Gwamanonin katsina da zamafara da Sokoto da Kebbi da kaduna da kano sun Tattauna muhimman batutuwa da su ka shafi matsalar rashin tsaron da talauci da dakushewar tattalin arziki wanda su ne manyan silar kawo matsalolin ta'addanci da garkuwan da mutanen da sauran miyagun laifuka da ake aiktawa.
Maigirma Ministan gidaje da Raya Birane na Najeriya Arch Ahmed Musa Dangiwa ya jadda bukatar samar da zaman lafiya a yankin Arewa maso yammacin Najeriya da hanyar samar da ayyukan yi ga matasa
.Manyan masana da kwararru a fannin tsaron daga cikin da wajen Najeriya jami'an ofishin jakadanci shugabanin hukumomin tsaron da sarakunan gargajiya da yan Siyasa da sauran masu ruwa da tsaki sun cimma Tattaunawa.
Muna rokon allah SWT ya zaunar da jiharmu lafiya da kasarmu baki daya Ammen ya hayyu ya kayyum
Hon.Habibu Adamu (Abba)
Chairman Dangiwa Media Reporters
25/06/2024