Da dumi dumi :Daga yayana, kanwata akeyi wu da.....
A wani lokaci wadanda ke zama kanwa uwar gami su jefa masoyi a cikin irin wannan hali su ne Cousin.
Daga yaya da kanwa ko tsokanar juna, sai Cousin su makale wa juna, su zame wa masoyan Cousin dinsu alakakai, kamar yadda aka yi wa Zara, ko da yake ta kwato abinta da kyar.
Matsalatar ta fi tsanani idan a gida daya aka taso ko dangantakar na da kusanci sosai tsakanin Cousin da masoyin mutum.
Shi ya sa yawancin masoya maza da mata ke ganin yayu ko kannen masoyansu na dangi a matsayin babbar barazana.
A al’adar Malam Bahaushe, ’ya’yan ’yan uwa abokan wasan juna ne, amma duk da haka, akwai iyaka tsakanin maza da ’yan uwansu mata, walau na kusa ko na nesa.
Sai dai yanzu zamani ya kawo yawaitar cudanya, saboda wasu dalilai, ciki har da kwaikwayon al’adun wasu kabilu, har ta kai ga wuce gona da iri a tsakanin Cousin da Cousin.
A wani lokaci hakan kan kai ga aikata abin kunya ko bacin rai, ko zama silar fasa aure ko mutuwarsa ko raba masoya ko yin fitsara ko aikata babban fasadi.
Aminiya ta tattaunawa da wasu don jin irin rawar da Cousin ke takawa a soyayya ko zamantakewar aure..